DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu Ya Cire Harajin kashi 5 Da Aka Sanya Kan Kuɗin Waya da Data a Najeriya

-

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya cire harajin kashi biyar (5%) da ake ɗora wa kan ayyukan sadarwa da suka gaɗa da kiran waya da Data a ƙasar nan. Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), Dr. Aminu Maida, ne ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa sabuwar dokar haraji da Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu a kai ta tabbatar da cire wannan nauyi daga kan ‘yan Najeriya.

A cewar Dr. Maida, cire wannan haraji zai rage wa masu amfani da wayar hannu da sauran ayyukan sadarwa nauyin kuɗi, wanda hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa rayuwa da kuma rage matsin lamba kan jama’a. Ya ce, wannan mataki ya yi daidai da manufofin gwamnati na sauƙaƙa rayuwar ‘yan ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Google search engine

Ya ƙara da cewa, cire harajin zai ƙara ƙarfin amfani da fasahar sadarwa a Najeriya, wanda hakan zai samar da ƙarin damar kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arziki. Haka kuma, ya nuna cewa gwamnati za ta ci gaba da duba hanyoyin da za su rage wa jama’a nauyin haraji a fannonin daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara