Jam’iyyar PDP ta yi gargadi cewa ba za ta yi jinkiri wajen hukunta duk wani mamba da ya saba wa kundin tsarin jam’iyyar ba, biyo bayan kalaman da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi kan babban taron ta na kasa da jam’iyyar ta shirya gudanarwa a watan Nuwamba.
A cikin wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Talata, Wike ya ce bai san da wani babban taro da za a yi ba, tare da jaddada cewa shi da abokan tafiyarsa za su kalubalanci duk wani abu da suka ga kamar rashin adalci ne.
Ya kuma yi korafi cewa ba a turo masa sanarwar taron kwamitin NEC ba, yana mai cewa zai kalubalanci tsarin idan bukatar hakan ta taso.
Sai dai mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya musanta ikirarin Wike, inda ya bayyana cewa an kira NEC bisa ka’ida, an turo sanarwa, kuma hukumar INEC ma ta samu takardar a hukumance.
Ologunagba ya tabbatar da cewa taron zai gudana a Ibadan, Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025, inda ya jaddada cewa shiri na tafiya yadda ya kamata.



