Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai karɓi baƙuncin sauran gwamnoni na jam’iyyar PDP a Gusau ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025.
Wannan taro dai na musamman ne da aka shirya domin tsara dabarun jam’iyyar tare da shiryawa babban taron kasa da za a gudanar a Ibadan, jihar Oyo, ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, taron zai zama wata dama ta tattaunawa kan manyan batutuwan siyasa, ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar, da kuma haɗa kai wajen ci gaban jihohin da gwamnoni ke jagoranta.
An bayyana cewa gwamnoni za su isa Gusau tun da yammacin Juma’a, inda Gwamna Dauda zai shirya musu liyafa kafin zaman da zasu gudanar a ranar Asabar.