DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Aliko Dangote ne mai kuɗin duniya na 88, a cewar sabon rahoton mujallar Forbes

-

Jerin sunayen masu kuɗi na duniya da mujallar Forbes ta fitar a karon nan ya nuna cewa ‘yan Najeriya hudu ne suka samu shiga cikin manyan attajirai a duniya.

A sahun gaba akwai Alhaji Aliko Dangote, wanda aka kiyasta dukiyarsa ta kai dala biliyan 24.4, yana matsayin na 88 a duniya.
Wannan ya ba shi tazara sosai daga sauran ‘yan Najeriya a jerin.

Google search engine

A bayan sa akwai: Abdulsamad Rabiu mai dala biliyan 7.2 da ke mataki na 516, sai Mike Adenuga mai dala biliyan 6.3 da ke matsayi na 592, da kuma Femi Otedola mai dala biliyan 1.5 wanda ke matsayi na 2,424.

Bambancin dukiya tsakanin Dangote da sauran abokan kasuwancinsa ta ninka adadin ta su Abdussamad Rabiu sau uku, ta fi ta Adenuga sau huɗu, sannan ta fi ta Otedola sau 16, kamar yadda binciken jaridar ya tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara