Wani na kusa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Atiku ya fi sha’awar ganin Najeriya ta gyaru fiye da burin zama shugaban ƙasa.
Maganar ta fito ne yayin taron karɓar sabbin masu sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC da aka gudanar a Legas ranar Asabar.
A cewar rahoton Punch mai dogaro da NAN, wasu manyan jiga-jigan jam’iyyun PDP da Labour Party ne suka sauya sheƙa zuwa ADC.
A wajen taron, Farfesa Ola Olateju daga Jami’ar Achievers da ke Owo, Jihar Ondo, wanda ya wakilci Atiku a wurin gangamin, ya bayyana cewa Atiku “ba ya azarbabin sai ya zama shugaban ƙasa, amma yana da kishin ganin Najeriya ta samu tsaro, ci gaba da kuma wadata.”
Rahotanni sun ce Atiku, tare da wasu ’yan adawa masu ra’ayi irin nasa, sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa ADC a shirye-shiryen fafatawa a zaben 2027.



