Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa maganar da shugaban rundunar tsaro Janar Christopher Musa, ya yi ba ya nufin kiran ‘yan ƙasa su ɗauki makamai su kare kansu.
Daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaro ta kasa, Brig. Janar Tukur Gusau, ya ce an yi kuskuren fahimtar maganganun CDS da ya yi a hira da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.
A cewarsa, Christopher Musa ya ƙarfafa ‘yan Najeriya ne su koyi dabarun kare kai da ɗaukar darussa irin su Taekwondo, Judo, Dambe, Iyo, da Tuƙi, ba wai yana kira su ɗauki makamai ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa duba asalin tushen magana kafin yada ta, tare da jaddada cewa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro na samun nasarori a yaƙi da rashin tsaro a fadin ƙasar.



