Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta bayyana cewa kimanin Naira biliyan 36 ta kashe a fannin tsaron jihar.
Kwamishinan tsaro cikin gida Dr Nasir Danmusa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a gidan gwamnatin jihar jim kadan bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.
A cewar gwamnatin yanzu jihar na da motocin sulke na APC guda 42 da wasu muhimman kayayyakin yaki domin kare al’ummar jihar daga yan fashin daji.
“Ko a safiyar Asabar dinnan mun ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su a dajin Fauwa” in ji Kwamishinan.
Kwamishinan ya kara da cewa yanzu jihar ta fara samun sauki daga hare-haren yan bindiga.
Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da hare-hare yan bindiga, ko a satin da ya gabata an hallaka mutane sama da 27 a kauyen gidan mantau dake karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.



