Gwamnatin sojin kasar Guinea ta dakatar da manyan jam’iyyun siyasa uku na tsawon watanni uku, ciki har da jam’iyyar tsohon shugaban ƙasa Alpha Condé.
Wannan mataki ya zo ne daidai lokacin da ake shirin gudanar da kuri’ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a ranar 21 ga Satumba, karkashin jagorancin Janar Mamadi Doumbouya wanda ya karɓi mulki a juyin mulki a shekarar 2021.
Rahotanni sun ce dakatarwar ta faru ne ’yan kwanaki kafin zanga-zangar da ’yan adawa suka shirya a ranar 5 ga Satumba, domin nuna adawa da mulkin Doumbouya.
Sai dai manyan jam’iyyu da ƙungiyoyin farar hula sun yi watsi da tsarin rubuta sabon kundin mulki, suna masu cewa wata hanya ce kawai ta ƙarfafa mulkin soja a ƙasar, kamar yadda DW Africa ta tabbatar.