Dakarun sojojin sama na Najeriya NAF sun kai farmaki a kan mafakar fitaccen ɗan bindiga Babbaro a Tudun Pauwa, Karamar Hukumar Kankara, inda suka ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da ƙananan yara.
A cewar Ma’aikatar tsaron cikin gida, sun dukkan mutanen da aka sace a lokacin harin da aka kai Unguwar Mantau da ke Malumfashi, sai dai an tabbatar da rasuwar yaro ɗaya a cikin lamarin.
Farmakin jiragen saman ya gudana tsakanin ƙarfe 6:00 zuwa 7:00 na yamma, inda aka kai hari kai tsaye kan mafakar danbindiga Babbaro, wacce ta dade tana zama barazana ga al’ummomin yankin.
Gwamnatin jihar Katsina ta jinjinawa dakarun hadin-gwiwar sojojin sama, sojin kasa da sauran hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ta fuskar kayan aiki, bayanan leƙen asiri da haɗin gwiwar al’umma domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.



