Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihohin Katsina da Zamfara, bayan hare-haren Malumfashi da suka yi sanadiyyar mutuwar gwamman mutane cikin watanni biyu.
Jam’iyyar ta ce kashe-kashen da suka hada da harbin mutane 30 a masallaci da kuma kona gidaje da mutanen ciki a Katsina, tare da sace-sacen jama’a a Zamfara, sun tabbatar da gagarumar gazawar tsarin tsaro.
Rahotonni da jaridar Punch ta tattaro hadakar jam’iyyar ta ADC Ta soki Shugaba Tinubu da zargin fifita yawon kasashen waje da daukar hoto maimakon kare ‘yan kasa, tare da jaddada cewa gwamnatin tarayya na bukatar sake duba tsarin tsaro da gaggawa.