Bukuwan da aka hana sun haɗa da Kauyawa day (Ranar kauyawa) da kuma Ajo party, inda samari da ‘yan mata kan yi ado da riga da wando marassa kyau tare da rawa daga yamma zuwa dare a matsayin bikin aure.
Wannan hukunci ya fito ne bayan amincewar da dukkanin manyan malamai masu jagorantar sallar Juma’a a Jalingo ƙarƙashin Majalisar Musulmi ta Jihar Taraba, tare da goyon bayan sarakunan gargajiya da hukumomi.
Ko a ranar Juma’ar da ta gabata, rahoton jaridar Daily Trust ya ce, wannan batun shi ne jigon hudubar da dukkanin malamai suka gabatar a masallatan Jummu’a na Jalingo.
Majalisar ta kuma yi gargadin cewa duk wani musulmi da ya karya wannan doka, babu wani limami da zai daura masa da auren sa, ya tsaya akan gawarsa yayin da ya rasu.
An kuma gargadi limamai da malaman addini cewa duk wanda ya saba wa wannan hukunci ya halarci jana’iza ko suna a gidan wanda ya karya doka, zai fuskanci hukunci ciki har da sauke shi daga muƙamin limanci.



