Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan yanar gizo da ke zargin cewa wasu makusantan gwamnati sun karkatar da kudi naira biliyan 6.5 daga baitul malin jihar.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin 25 ga Agusta, 2025, gwamnati ta ce rahoton da aka wallafa a shafin Daily Nigerian a ranar 22 ga watan nan, ya yi nuni da cewa Babban Darakta a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Rogo, na cikin shari’ar da ake yi kan zargin karkatar da kudaden.
Sanarwar ta ce gwamnati ba za ta yi katsalandan a shari’ar da ke gaban kotu ba, amma dole ne ta fayyace wa jama’a cewa duk kudin da ake fitarwa daga ma’aikatu ko hukumomi a jihar na tafiya ne bisa tsarin kasafin kudi da kuma umarnin gwamnati, ba tare da wata damar daidaikun mutane su yi amfani da kudaden jama’a ba.
Ta kara da cewa ofishin daraktan na da manyan nauyuka da suka hada da jigilar baƙi, masauki, da shirya tarurruka na gwamnati da kuma gudanar da wasu muhimman ayyuka na Gwamna a cikin gida da waje, lamarin da ke bukatar kashe makudan kudade.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana da cikakken kwarin gwiwa kan gaskiya da nagartar Alhaji Abdullahi Rogo, tare da zargin cewa masi adawa ne ke ƙoƙarin bata sunan jami’an gwamnati da kuma karkatar da hankalin jama’a daga nasarorin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke samu.
Sanarwar ta kuma tunatar da jama’a yadda gwamnatin da ta gabata ta kashe sama da naira biliyan 20 a cikin watanni uku kacal kafin ta bar mulki, tare da ambaton badakalar bidiyon dala da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin ta ce ba ta da abin ɓoyewa, domin kowanne jami’in gwamnati, na da cikakken shiri na bayyana wa hukumomin bincike duk wani abu da ya shafi aikinsa idan an bukata.
Daga karshe, gwamnatin Kano ta shawarci ’yan adawa da su daina yaɗa labaran ƙarya da ƙage domin neman yin barna a siyasa, tare da gargadin cewa za ta dauki matakin doka kan duk wanda ya ci gaba da bata sunan jami’anta ba bisa hujja ba.