Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF ta gargadi cewa Arewacin Nijeriya na kara shiga mawuyacin hali sakamakon tabarbarewar tsaro, talauci da matsalolin muhalli.
Kungiyar ta fitar da wannan gargadi ne a yayin taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 78 da ta gudanar a Kaduna.
Shugaban ACF, Mamman Osuman, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa Arewa ba za ta iya ci gaba da yin shiru ba a yayin da matsalolin da suka dabaibaye yankin ke kara ta’azzara.