Aƙalla mambobin Majalisar Wakilai 48 da Sanatoci 5 sun kasa shiga wata muhawara, daukar nauyin kudurori ko gabatar da koke-koke a majalisar dokoki cikin tsawon watanni 12, a cewar wani sabon rahoto da aka fitar a ƙarshen mako.
Rahoton ya fito ne daga Deliberative Barometer and Policy-Focus Productivity Report (NASS-DBPFR), wanda Erudite Growth and Advancement Foundation (ERGAF-Africa) ta wallafa, inda aka bibiyi ayyukan majalisa daga ranar 14 ga Yuni, 2023 zuwa 13 ga Yuni, 2024.
A cewar rahoton, waɗannan ‘yan majalisar ba su yi ko da ɗaya daga cikin ayyukan zaman majalisa ba a lokacin da aka duba. An jaddada cewa gazawarsu na shiga muhawarar majalisa ko daukar nauyin kudurori na rage ingancin doka da kuma saɓa tsarin mulkin dimokuraɗiyya.