Babban jami’an tsaron kasar Japan ya ba da hakuri ga iyalan wani ɗan kasuwa da aka kama bisa kuskure kuma ya rasu bayan watanni da dama yana tsare.
Shizuo Aishima, tsohon mai ba da shawara ga kamfanin kera injuna Ohkawara Kakohki, na daga cikin shugabannin kamfanin guda uku da aka tsare ba bisa ƙa’ida ba kuma ba tare da hukunci ba na watanni da dama kan tuhumar da daga bisani aka soke.
’Yan fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam sun daɗe suna kira da a kawo ƙarshen abin da ake kira da adalci a Japan, inda masu bincike ke amfani da tsare-tsare na dogon lokaci kafin shari’a domin tilasta wa mutum ya amsa laifi.