Jikanyar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Halima Amira Junaid, za ta amarce da angonta Walid Shehu Mauzu a Jihar Kaduna.
Halima ita ce ’yar Nana Hadiza, wadda Abubakar Malami SAN ya aura shekaru kaɗan da suka wuce.
Hadiza ita ce diyar Buhari a aurensa na baya, kuma yanzu ita ce matar Malami ta uku. A baya ta yi aure da Junaid, inda ta haifi ’ya’ya guda shida.
An shirya gudanar da ɗaurin auren Halima da Walid a ranar 30 ga watan Agusta, 2025.