Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaben shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne ta bakin ɗaya daga cikin masu magana da yawunsa a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Tunde Olusunle.
Yayin da yake magana da jaridar ThisDay, Olusunle ya ce Atiku zai sake tsayawa takara a 2027 domin ceto Najeriya daga halin da ta shiga a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.