Rahotanni da gidan talabijin na Channels ya tattaro sun nuna cewa wani jirgin ƙasa da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya fadi daga kan layi a safiyar Talata, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin tashin hankali da firgici.
Shaidun gani da ido daga cikin jirgin sun bayyana cewa mutane sun ruga neman dauki daga jama’a cike da rudewa.
Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin hatsarin ba, haka kuma babu tabbacin ko an sami raunuka ko asarar rayuka.
Hukumar tsaro ta ce an tura dakarun soji zuwa wurin domin taimaka wa wajen fitar da fasinjojin da suka makale.