Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Delta ta tabbatar da kama wasu jami’anta da suka bayyana a bidiyo suna lissafin dimbin kuɗi a cikin motar sintiri mai alamar Area Command Asaba.
Bidiyon ya bazu a shafukan sada zumunta, inda jama’a suka yi zargin cewa kuɗin na iya zama irin na goro da wasu jami’ai kan karba a manyan hanyoyi ko na kwace.
Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun rundunar, Bright Edafe, ya tabbatar da cewa an gano jami’an, an gurfanar da su gaban kwamishinan ’yan sanda, sannan an ɗauki matakin dakatarwa da tsarewa.
Ya ce tuni rundunar ta tura manyan jami’an biyu sashen tuhuma, yayin da sauran su biyun, masu mukamin Inspector kuma ake tsare da su don fuskantar shari’a a cikin gida, wacce ke matsayin tsarin ladabtarwa a rundunar.
Comment:Wannan ai ba sabon abu bane, cin hanci wurin yan sanda ya zama jiki.