Yan bindiga dauke da makamai sun shiga cikin garin Katsina a daren ranar Litinin a wata unguwa Filin Kanada sabuwar unguwar Kofar kaura dake tsakiyar birnin jihar.
Makwabcin wanda iftila’in ya shafa, ya kuma bukaci a sakaya sunansa, ya shaida ma DCL Hausa yadda lamarin ya faru.
A cewar sa, wasu da ake zargin yan fashin daji ne sun sace makwabcin sa mai suna Anas Ahmed da maidakinsa Halimatu da kuma diyarsu.
Maharan sun ziyar ci unguwar da misalin karfe 3:00 na dare kuma sun hallaka wani danbanga nan take, wanda yake aikin tabbatar da tsaro a yankin.