Kakakin tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje ya musanta sabbin zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamnan Kanon cewa tare da cewa an gina tuhumar ne a doron siyasa ba gaskiya ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin dinnan Garba wanda tsohon kwamishinan yada labarai ne a jihar Kano ya ce gwamnatin Kano na ƙoƙarin haɗa Ganduje da badakalar kuɗi, cin hanci da kuma mallakar filaye ba bisa ka’ida ba.
A ranar Litinin gwamna Abba Kabir Yusuf ya zargi Ganduje da kashe fiye da Naira biliyan 20 tsakanin watan Fabrairu da Mayun 2023, bayan APC ta sha kaye a hannun jam’iyyar NNPP.