Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta bayyana cewa duk da amincewar shugabanninta da gwamnoninta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tazarce, ba za a hana sauran ’yan jam’iyya neman tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.
Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na kasa, Sulaiman Mohammad Argungu, ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce jam’iyyar za ta fitar da sahihin ɗan takara, kuma duk mai sha’awa zai iya sayen fom.
Ya ce amincewa da Tinubu ba yana nufin an rufe ƙofa ba ne, illa dai yabo ga ayyukan sa da suka sa ya cancanci tazarce.
Argungu ya ƙara da cewa nasarar APC a kujeru 13 daga cikin 16 a zaben cike gurbi na baya-bayan nan kwarin gwiwa ne daga jama’a kan ingancin shugabancin jam’iyyar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito shi.