A safiyar Laraba, wasu gungun shugabannin matasan Niger Delta sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin NNPCL a Abuja, inda suka toshe ƙofofin shiga da fita na ginin tun misalin ƙarfe 6 na safe.
Rahotanni da jaridar Punch ta tattaro sun ce masu zanga-zangar dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce suna zargin Shugaban NNPCL, Bashir Ojulari, da cin hanci da rashin iya gudanar da aiki, tare da neman ya yi murabus.
Haka kuma, sun bukaci a nada ɗan asalin yankin Niger Delta a matsayin sabon shugaban kamfanin.
‘Yan sanda da jami’an tsaro sun sun yi dafifi a wurin domin tabbatar da kwanciyar hankali da kuma karkatar da zirga-zirgar ababen hawa zuwa wasu hanyoyin na daban.
An tilasta ma’aikatan kamfanin da dama ajiye motoci a nesa daga ginin saboda toshe hanyoyin shiga da masu zanga-zangar suka haifar.