Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Kaduna ta yaba wa gwamna Uba Sani kan matakin mayar da wasu daga cikin malaman da gwamnatin baya ta Nasir El-Rufai ta kora sama da dubu 23 a tsakanin shekarun 2018 zuwa 2021.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaban NLC na jihar, Ayuba Suleiman, ya bayyana haka yayin taro da kungiyar ’yan jarida, inda ya ce gwamnatin yanzu ta fara maido da shugabannin makarantu, ma’aikatan gudanarwa da malaman kimiyya da abin ya shafa.
Ya ce gwamnatin Uba Sani na kokarin gyara kura-kuran da aka tafka a baya, tare da tabbatar da ganin ba’a ci gaba da tauye hakkin ma’aikata ba.
A cewar Suleiman, gwamnatin ta kuma amince da sabon mafi karancin albashi na Naira dubu 72 ga ma’aikatan da ke mataki na daya zuwan a bakwai.