Jam’iyyar NNPP, ta aika da takarda zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, tana bukatar a dakatar da dukkan zabubbuka a Najeriya har sai an sanya sahihin tambarinta a kan takardun kada kuri’a.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito lauyan jam’iyyar, Ndubuisi Ukpai (Esq), ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya rubuta wa shugaban INEC, ranar 25 ga watan Agusta.
Ya ce dole a tabbatar da sahihin jagoranci na Dr. Major Agbo a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa kafin ci gaba da gudanar da zabukan gama gari a kasar.
NNPP ta zargi INEC da kin bin hukuncin kotuna da suka tabbatar da shugabancin Agbo, lamarin da ya sa jam’iyyar ta nemi kotu ta tilasta hukumar bin doka.
Jam’iyyar ta jaddada cewa har sai an gyara batun tambari da jagoranci, bai kamata INEC ta gudanar da wani zabe a kasar ba.