Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sanata Abba Moro, ya amince cewa jam’iyyar ta yi kuskure wajen tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.
Moro ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya ce wannan mataki ya raunana damar jam’iyyar a zaɓen da ya gabata.
Ya bayyana cewa PDP ta yi adalci a wannan karo da ta amince da tsayar da ɗan takara daga kudu a zaɓen 2027, yayin da arewa za ta ci gaba da rike shugabancin jam’iyyar na kasa.