Jam’iyyar ADC ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira “ƙididdiga marar ma’ana” da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijeriya INEC ta fitar game da sabbin masu rijista a makon farko na aikin rijistar da ake yi.
A cewar jam’iyyar, rahoton ya nuna cewa a jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya musamman Osun, an samu kusan sabbin rijista 400,000 cikin mako guda, adadi da ya sha banban da tarihin baya da kuma gaskiyar yawan jama’ar jihar.
A cikin sanarwar da Malam Bolaji Abdullahi, Sakataren yaɗa labaran ADC na ƙasa ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta yi gargaɗi cewa irin waɗannan alkaluma masu cike da shakku na iya lalata amincewa da tsarin zaɓen Najeriya baki ɗaya idan ba a yi karin bayani ba.
Jam’iyyar ta yi nuni da cewa abin mamaki ne yadda yawan masu rijistar mako guda a Osun ya fi gaba ɗaya waɗanda aka samu a cikin shekara huɗu da suka gabata.
Haka kuma, yankin Kudu maso Yamma kawai ya dauki kashi 67 cikin 100 na sabbin masu rijistar a ƙasa baki ɗaya.
ADC ta bukaci INEC ta fito fili ta bayyana yadda hakan ya kasance, tare da tabbatar da cewa ba a karkatar da tsarin rijistar masu kada kuri’a ba.