Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin takara a kowanne mukamin siyasa a zaben 2027.
Ya ce komawarsa cikin harkokin siyasa ba don wani muradin kansa ba bane, illa dai don goyon bayan shugabanci na gari a kowane mataki na gwamnati.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, El-Rufai ya yi wannan bayani ne a Kaduna, yayin taron tarbar wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka koma jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Aliyu Bello.
Ya ce tun bayan saukarsa daga mulki a 2023, burinsa shi ne ya huta daga siyasa, amma abubuwan da suka faru a kasar nan sun sa ya koma, don ya tallafa wa matasa, mata da kuma masu kishin sauyi a siyasa.