’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu ma’aurata da ’yarsu a unguwar Filin Canada Quarters da ke Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina, sun nemi Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa.
Wata majiya daga cikin iyalan, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana wa Daily Trust cewa masu garkuwar sun kira ta hanyar lambar waya ta Anas Ahmadu, wanda shi ne mijin da aka sace.
Anas Ahmadu mai shekaru 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda, aka yi garkuwa da su tun ranar Talata da safe.
A yayin harin, wani ɗan sa-kai mai suna Abdullahi Muhammad (25) ya rasa ransa bayan da aka harbe shi yayin ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.