DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Kebbi Nasiru Idris ya naɗa sabon Sarkin Zuru

-

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya amince da naɗin Sanusi Mika’ilu-Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru.

Mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris, ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi a ranar Alhamis.

Google search engine

Jaridar Daily Nigerian ta ambato kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu ta jihar, Garba Umar-Dutsin-Mari, na sanar da naɗin, yayin da ya mika takardar tabbatarwa ga sabon sarki a Zuru.

Kwamishinan ya ce daga cikin ƴan takara uku da suka nemi kujerar, bayan kwamitin zaɓen masarautar ya tantance su, Sanusi Mika’ilu-Sami ne ya samu mafi yawan ƙuri’u da suka ba shi damar hawa gadon sarautar Zurun.

An naɗa shi ne sakamakon rasuwar tsohon Sarkin Zuru, Muhammad Sani-Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke Landan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yadda na rasa ɗiyata da jikokina sanadiyyar shan ‘Dettol’ a matsayin magani

Rashin sani ya haddasa mutuwar yata da jikokina bayan da suka sha Dettol a matsayin magani Wata dattijuwa mai suna Asiya Hassan da ke zaune a...

Shugaban Sashen Hausa na BBC Aliyu Tanko ya ajiye aiki

Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ajiye aikinsa bayan ya shafe shekaru 17 yana aiki da gidan. Tanko, wanda ya zama babban...

Mafi Shahara