Gwamnatin Nijeriya ta ba Nafisa Abdullahi ‘yar asalin jihar Yobe da ta zo na daya a gasar Turanci ta Duniya kyautar kudi Naira 200,000.
Ministan ilmin Nijeriya Mr Tunji Alausa ne ya sanar da wannan kyauta a wani biki da aka gudanar a Abuja kamar yadda jaridar Punch ta rawaito
A baya dai gidauniyar Atiku Abubakar ta bai wa zakarun TeenEagle wato Nafisa Abdullahi, Rukaiya Fema, da Khadija Kalli tallafin karatu sakamakon bajintar da suka yi a gasar TeenEagle ta duniya.