Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya jagoranci taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) a yau Alhamis a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Taron ya samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, da kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, wanda shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma.
Haka zalika, gwamnoni daga jihohin Zamfara, Jigawa, Legas, Anambra, Gombe, Imo, Akwa Ibom, Cross River, Benue da Ondo sun halarci taron, tare da gwamnan rikon na Jihar Rivers.
Taron NEC din na yau a cewar rahoton gidan talabijin na Channels ya gudana ne kan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin ƙasa da manufofin gwamnatin Tinubu.