Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwa kan rushe-rushen da gwamnatin Legas ta yi a kasuwar Hausawa ta Alaba Rago da ke Legas, inda ta kira lamarin da babban koma baya ga dubban ‘yan kasuwar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta na ƙasa, Farfa T. A. Muhammad-Baba, ya sanya hannu, kungiyar ta ce duk da cewa babu rayuka da aka rasa, rushewar ya jefa iyalai da dama cikin ƙunci bayan salwantar kadarori da kasuwanci.
Jaridar Daily Trust ta ambato cewa, kungiyar ta kuma jajantawa wadanda abin ya shafa tare da kiran su yi hakuri wajen fuskantar lamarin.
ACF ta kuma nemi ƙarin bayani kan lamarin domin shiga tattaunawa da gwamnatin jihar Legas da al’ummar da abin ya shafa, domin a sami mafita mai kyau.