Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya gana da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a birnin Paris, domin ƙasashen biyu su ƙarfafa dangantaka a fannonin zuba jari, kasuwanci, tsaro da harkokin soja.
Taron ya zo ne makonni kaɗan bayan Faransa ta rufe sansanoninta na soja na ƙarshe a Senegal, wanda ya kawo ƙarshen sama da shekaru 60 da kasancewar dakarun Faransa na dindindin a ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Shugaba Diomaye Faye ya bayyana cewa ƙasashen biyu za su sake nazarin yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a babban taron gwamnati-zuwa-gwamnati na gaba, da za a gudanar a watan Satumba a birnin Dakar.