Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyarsa ta sake gina martaba da kimar Najeriya a idon duniya, inda ya ce wannan nauyi ne da ’yan Najeriya suka dora masa a zaɓen 2023.
Tinubu ya bayyana hakan ne bayan dawowarsa Abuja a safiyar Alhamis, daga ziyarar aiki ta makonni biyu da ya kai ƙasashen Japan da Brazil.
A cewar sa, duk wata tattaunawa da yarjejeniya da aka cimma a waɗannan ƙasashe an yi su ne da manufar samar da damarmaki da za su kawo ci gaban tattalin arziki, ƙirƙirar ayyukan yi, da inganta walwalar al’ummar Najeriya.
Ya ƙara da cewa a Japan Najeriya ta kulla yarjejeniyoyi da za su kawo sababbin hannun jari a fannoni inganta masana’antu, fasaha, da habbaka tattalin arzikin kan yawan jama’a.
A Brazil kuwa, ya ce an zurfafa alaƙa a harkokin kasuwanci, noma, jiragen sama, da harkokin kuɗi, tare da ganawa da shugabannin masana’antu domin ƙara tabbatar da amincewa da tattalin arzikin Najeriya.