Rahotanni daga Mexico sun bayyana cewa wasu ’yan majalisar dokoki na ƙasar sun rika musayar naushi a a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba, bayan muhawara mai zafi kan zargin da aka yi cewa ’yan adawa sun nemi sojojin Amurka su shiga ƙasar domin yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga shafukan sada zumunta na majalisar ya nuna ɗan majalisar daga tsagin adawa Alejandro Moreno daga jam’iyyar PRI yana ture shugaban majalisar, Gerardo Fernandez Norona na jam’iyyar mai mulki Morena, har ma ya mare shi a wuya sannan ya ture wani ɗan majalisa da ya shiga tsakani.
Rahotanni daga kafofin watsa labaran Amurka sun nuna tsohon Shugaban ƙasa Donald Trump ya nemi sojojin Pentagon su ɗauki mataki kan ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi a Latin Amurka da ake kira ta’addanci, sai dai gwamnatin Mexico ta ce ba za ta taɓa amincewa da shigar sojojin Amurka a ƙasar ba.