An kama wani jami’in ‘yan sanda da ake zargi da harbin soja har lahira a ƙauyen Futuk, Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Mai rikon mukamin daraktan hulɗa da jama’a na sojoji a 33 Artillery Brigade, Atang Hallet Solomon, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’in ya shiga hannun hukuma kuma ana ci gaba da binciken hadin gwiwa tsakanin sojoji da ’yan sanda.
Rahotanni da jaridar Daily Trust ta tattaro daga wasu mafarauta da jami’an sa-kai sun nuna cewa rikicin ya biyo bayan takaddama tsakanin jami’an tsaro kan wani motar ɗaukar ma’adinai da ake zargin ta fito daga wurin hakar ma’adinai na kamfanin wasu ‘yan kasar China a yankin Yalo.