Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon ministan sufurin jiragen kasa a Nijeriya, Rotimi Amaechi, ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 karkashin jam’iyyar ADC.
Jaridar Punch ta ruwaito Amaechi ya bayyana haka ne a Kano, lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan wani taro da ya yi da gamayyar ’yan kasuwa.
Ya ce ba zai janye wa wani ɗan takara ba a zaben fid-da-gwanin jam’iyyar, inda ya jaddada cewa wajibi ne jam’iyyar ADC ta ajiye takarar a fili domin tabbatar da dimokuradiyyar cikin gida.
Ya kuma soki gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa ’yan Najeriya sun gaji da manufofinta, da ke sabbaba talauci da matsin rayuwa ke kara kamari a fadin kasar.