Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta tsayar da ɗan takarar shugaban kasa daga Kudancin Najeriya wanda yake Kirista a zaɓen 2027.
Mohammed ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels T ranar Alhamis.
Ya ce PDP ta koyi darasi daga kuskuren da jam’iyyar APC ta yi a zaɓen 2023, lokacin da ta tsayar da tikitin addini ɗaya (Muslim-Muslim ticket).
Gwamnan Bauchi ya kuma musanta jita-jitar da ke cewa PDP na shirin tsayar da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin ɗan takarar shugaban kasa tare da sanya shi a matsayin mataimaki.



