Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa takarar shi da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, za ta yi armashi idan jam’iyyar PDP ta tsayar da su a matsayin ‘yan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Mohammed ya bayyana haka ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya karyata jita-jitar cewa tuni aka tsayar da shi a matsayin mataimakin Makinde. Sai dai ya ce wannan zaɓi na nan a buɗe a hannun PDP.
Rahoton jaridar Punch ya ruwaito shi yana bayyana cewa dole jam’iyyar ta tsayar da ɗan takara Kirista daga Kudancin Najeriya tare da ɗan takara Musulmi daga Arewa domin nuna bambancin ƙasa da guje wa cece-ku-cen da tsarin Muslim-Muslim ticket ya jawo wa APC a baya