An gano gawar wani matashi mai shekara 29 da ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a a karamar hukumar Shagari ta jihar, a jirgin da ya dauki mutum 11, inda tuni aka ceto mutum 9 yayin da ake neman wata dattijuwa.
Mai bai wa Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman a hukumar SEMA ta jihar, Aminu Bodinga, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce hatsarin ya afku ne ranar Alhamis.
Ya kara da cewa jami’an SEMA sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto da kuma binciken wadanda suka bata.

Ana ci gaba da neman wata dattijuwa bayan kifewar kwale-kwale dauke da fasinja 11 a Sokoto
-