Jihar Legas ta fi kowace jiha amfana da manyan ayyukan da majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) ta amince da su, waɗanda suka kai naira tiriliyan 3.9.
Wannan adadi ya ninka da kashi 111 cikin ɗari na jimillar naira tiriliyan 3.56 da aka amince da su ga Yankin Kudu maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, waɗanda ke haɗa jihohi 18 baki ɗaya cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a cewar binciken Daily Trust.
Binciken ya gano cewa a cikin wannan lokaci, FEC ta amince da ayyuka masu darajar:
Naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma,
Naira tiriliyan 2.41 ga Kudu maso Kudu,
Naira biliyan 407.49 ga Kudu maso Gabas,
Naira tiriliyan 1.15 ga Arewa ta Tsakiya (ciki har da Abuja),
Naira tiriliyan 2.7 ga Arewa maso Yamma,
Naira biliyan 403.98 ga Arewa maso Gabas.
Haka kuma, an amince da naira tiriliyan 2.70 don manyan titunan da ke ratsa yankuna daban-daban, sai dai ba a fayyace rabon kowanne yanki ba.
Jimillar kwangilolin da FEC ta amince da su a wannan lokacin sun kai kusan naira tiriliyan 15.79.



