Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya janye ikirarin da ya yi a baya cewa babu wata yarjejeniya mai tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, inda yanzu ya amince cewa yarjejeniyar 2009 ta FGN-ASUU tana nan daram.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ministan ya bayyana cewa yarjejeniyar ta shekarar 2009 na nan a matsayin ingantacciya kuma mai ɗaurewa har zuwa yau.
Wannan karin haske ya biyo bayan jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, inda ya yi watsi da matsayar ASUU a matsayin takardar daftari kawai, yana mai jaddada cewa babu wata yarjejeniya da aka taɓa sanya hannu a kanta, abin da kungiyar ta yi gaggawar ƙalubalanta.
A cewar ministan, yarjejeniyar 2009 da 2011 da ASUU ke yawan ambato, “ba a taɓa sanya hannu a kansu ba, sai dai shawarwari ne da aka gabatar yayin tattaunawa.”
