Rikicin siyasa na ƙara kamari a jihar Kaduna bayan jam’iyyar ADC ta nesanta kanta daga wani taron da aka danganta da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan zarge-zargen tashin hankali da harbe-harbe a wajen taron.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ADC na jihar Kaduna, Injiniya Musa Idris, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, jam’iyyar ta karyata abin da aka kira kwamitin wadanda suka sauya sheka daga APC, PDP, SDP, LP, NNPP zuwa ADC, da aka ƙaddamarwa.
Jam’iyyar ta jaddada cewa El-Rufa’i ba ɗan ADC bane, don haka bai da wani hurumin shirya taruka a madadinta.
A gefe guda kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa ta fara binciken lamarin bayan samun rahoton cewa ‘yan daba sun yi ɓarna a wajen taron siyasar.

ADC ta nesanta kanta da Nasiru El-Rufa’i bayan taron jam’iyyar da aka yi tashin hankali a Kaduna
-
Comment:El-rufa’i ya sami matsala.