Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da aka gudanar a ranar Asabar.
Ita kuwa jam’iyyar da ke mulki a jihar wato PDP, ta samu nasara a kananan hukumomi uku kacal a zaɓen da hukumar zaɓen mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta gudanar.
Gwamna Siminalayi Fubara ma ya sha kaye a mazabarsa ta karamar hukumar Opobo-Nkoro inda babbar jam’iyyar adawa ta jihar ta yi nasara.
Shugaban RSIEC, Dr. Michael Odey, ne ya bayyana sakamakon a ofishin hukumar da ke kan titin Aba Road a birnin Fatakwal, a ranar Lahadi da rana.
