DCL Hausa Radio
Kaitsaye

SERAP ta soki gwamnatin Tinubu game da karin fasfo

-

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da adalci da shugabanci nagari ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta soke ƙarin kuɗin fasfo da hukumar shige da fice ta sanar, wanda tace anyi ba bisa ka’ida ba.

A cewar sanarwar da mataimakin daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, wannan sabon ƙarin kuɗin zai toshe wa miliyoyin talakawa damar samun fasfo mai shafuka 34 na shekaru 5 da mai shafuka 64 na shekaru 10.

Wannan ne karo na uku cikin shekaru biyu da ake yin ƙarin kuɗaɗen fasfo, kuma zai fara aiki a watan Satumba 2025 kafin.

A bara, cikin watan Agusta 2024 aka yi irin wannan karin kudin fasfon a Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili shi ne Mataimakin Editan Gudanarwa kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki na DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Jam‘iyyar APC ta lashe kujeru 20 cikin 23 a zaben kananan hukumomin jihar Rivers

Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da aka gudanar a ranar Asabar.Ita kuwa jam’iyyar...

Mafi Shahara