DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu adali ne, bai fifita kowane yanki ba wajen rarraba ayyukan ci-gaba ba a Nijeriya – Gwamnatin tarayya

-

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gudanar da mulkinsa bisa gaskiya da adalci wajen rabon ayyuka, mukamai da damar ci-gaba ga dukkan sassan ƙasar.

Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ne ya fitar da wannan jawabi a yau Lahadi, inda ya ce duk maganganun da ake yadawa kan nuna wariya a rabon ayyuka ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, manyan ayyukan gina hanyoyi, jirgin ƙasa, da lantarki suna gudana a lokaci guda a yankunan Arewa da Kudu.

“Daga cikin rarraba ayyuka, Arewa maso Yamma ce ta fi cin gajiyar kudade da sama da ₦5.9 tiriliyan, sannan ta biyo da Kudu maso Kudu da ₦2.4 tiriliyan, Arewa ta Tsakiya ₦1.1 tiriliyan, Kudu maso Gabas ₦407 biliyan, Arewa maso Gabas ₦400 biliyan, sai Kudu maso Yamma da ₦604 biliyan banda Legas” in ji ministan.

Idris ya ce gwamnati ta kuma sake farfado da aikin tashar wutar lantarki ta Kaduna, aikin gas na AKK, da hako man fetur a yankin Kolmani. Ya kara da cewa an gyara cibiyoyin kiyon lafiya sama da 1,000 domin inganta walwalar jama’a.

Ya ce, “Shugaba Tinubu ba ya gina kayan alfahari na gari guda, amma yana ginawa ƙasa baki ɗaya. Duk yankuna na da adalci da dama.”

Ministan ya kuma jaddada cewa shugaban kasa yana bin tsarin bai wa kowane yanki wakilci a cikin mukaman gwamnati, yana mai tabbatar da cewa babu wani bangare da aka bar baya a cikin Renewed Hope Agenda.

Google search engine
Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili shi ne Mataimakin Editan Gudanarwa kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki na DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

1 COMMENT

  1. Gaskiya a nan dai sai muce Ministan yayi mana qarya. Idan yana maganar cewa wai Arewa Maso Yamma tafi amfana da Ayyukan Raya Kasa, to sai muce masa mu ba Jahilai bane domin kuwa Ayyukan da yake magana akansu tun na Tsohuwar Gwamnati ne. Kuma munsan yadda tsarin kwangilar ya gudana, don haka babu wani aiki ko da na Kwatankwacin N100K, da za’a yi mana Qaryar amma na shi balantana har na 5.9TR. Ku bari 2027 tazo a nan ne zaku ga sakamakon Qaryar da kuke mana

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Mafi Shahara