DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsayar da Good Luck Jonathan ko Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban kasa ba alheri ne ga PDP ba – in ji wani ministan Tinubu

-

Ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya Festus Keyamo, ya gargadi jam’iyyar PDP cewa tana iya fuskantar babban koma baya a shirin ta na tunkarar 2027, idan har ta tsayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ko kuma tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, a matsayin ɗan takara.

A wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Keyamo ya ce jam’iyyar adawar tana cikin “hali mai rauni” tun bayan da ta kasa tsayar da tikitin shugabancin ta na 2023 ga yankin Kudu — abin da ya ce ya sa PDP ta rasa goyon baya a wuraren da take da karfi a baya kamar Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Keyamo ya bayyana cewa tsayar da Jonathan ɗan takara na iya haifar da cikas na doka bisa sashen 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ya nuna cewa duk wanda aka rantsar sau biyu a matsayin shugaban ƙasa ba zai sake tsayawa takara ba.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta ɗauki alhakin kawar da ido kan wannan batun idan ta tsayar da shi sannan daga bisani aka soke takararsa bayan an rufe tsayar da ɗan takara.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili shi ne Mataimakin Editan Gudanarwa kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki na DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Mafi Shahara