Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a shekarar 2027 ba.
Wike, wanda tsohon Gwamnan Jihar Rivers ne, ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce duk da cewa jam’iyyar PDP ta kebe tikitin takarar shugabancin ƙasa ga yankin Kudu, bai dace ya tsaya takara ba a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya naɗa shi a mukamin Minista.
Wike ya ƙara da cewa wannan matsaya tasa ba ta da alaƙa da neman dama a siyasa, sai dai ya yi haka ne domin biyayya da kuma ka’ida.
Haka zalika, tsohon gwamnan ya bayyana cewa da ba don ƙaunar da yake yi wa jam’iyyar PDP ba, da tuni ta shuɗe.



