DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Kaduna ta yi wa El-Rufai gargaɗi na ƙarshe da kuma zarginsa da kokarin tayar da hankalin jihar

-

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai gargadi tana zarginsa da shirin tayar da hankalin jihar a ƙarƙashin mulkin Gwamna Uba Sani.

A cikin wata hira da aka yi da El-rufa’i a cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya da ta Kaduna sun biya ’yan bindiga makudan kudade a matsayin wani ɓangare na bin matakin sulhu da ake ɗauka don kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Google search engine

Sai dai Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya musanta wannan ikirari a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna, Suleiman Shuaibu, ya sanya wa hannu, gwamnatin jihar ta ce ba za ta zura ido ta bari tsohon gwamnan, wanda ta zarga da barin jihar cikin hali na tabarbarewa, ya jawo rikice-rikice da tayar da tarzoma ba.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta ga dole ta yi wannan gargaɗi na ƙarshe ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wanda ta zarga da ƙoƙarin haifar da rikici a jihar, da nufin dagula lamurra da maida Kaduna zuwa tsohon yanayi na rikicin kabilanci da addini, rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki.

1 COMMENT

  1. Wannan duk Hauragiya ce Gwamnatin Kaduna take yi da kuma Tarayya, mu Talakawa muna mun zura musu Ido suyi su gama. Mu fatanmu shi ne Ubangiji Allah ya nuna mana 2027 lfy. Za su kwashi Zubin Adashen da suka yi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara